22 Yuni 2020 - 09:39
​ECOWAS Ta Bukaci A Sake Gudanar Da Wasu Zabuka A Kasar Mali

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta bukaci Mali ta sake gudanar da wasu daga cikin zabukan sassan kasar da sakamakonsu ya tunzura al’umma wanda ya kai ga zanga-zangar bukatar murabus din shugaba Boubacar Keita a Juma’ar da ta gabata.

(ABNA24.com) -  Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta bukaci Mali ta sake gudanar da wasu daga cikin zabukan sassan kasar da sakamakonsu ya tunzura al’umma wanda ya kai ga zanga-zangar bukatar murabus din shugaba Boubacar Keita a Juma’ar da ta gabata.

Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, sanarwar da ECOWAS ta fitar ta bukaci gwamnatin kasar ta Mali da ta sake yin dubi cikin tsanaki kan sakamakon zabukan na dukkanin yankuna da sassan kasar, tare da sake gudanar da wasu daga ciki domin kawo karshen rikicin siyasar da hakan ya haifar.

Bukatar ta ECOWAS na zuwa kwana guda bayan Sakatare Janar na Majlisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress ya bukaci bangarorin adawa da su ja hankalin magoya bayansu domin gujewa fadawar kasar cikin wani sabon rikici.

Dubun dubatar al’ummar kasar ta Mali ne dai suka gudanar da wata gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnati a Juma’ar da ta gabata, inda suke bukatar shugaban kasar Bubakar Keit daya yi murabus, yayin da shi kuma ya bayyana shirinsa na zama kan teburin tattaunawa da masu boren, domin jin korafe-korafensu.



/129